logo

HAUSA

Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin za ta aiwatar da ayyuka 9 da aka cimma a gun taron ministoci na FOCAC na wannan karo

2021-12-02 20:36:44 CRI

Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin za ta aiwatar da ayyuka 9 da aka cimma a gun taron ministoci na FOCAC na wannan karo_fororder_afirka

Daga ranar 29 zuwa 30 ga watan Nuwanba ne, aka gudanar da taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC a kasar Senegal cikin nasara, inda bangarorin Sin da Afirka suka tsara burin da suke fatan cimmawa nan da shekarar 2035 a hadin gwiwar dake tsakaninsu. A yayin taron manema labaru da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta gudanar a yau, kakakin ma’aikatar Shu Yuting ta bayyana cewa, Sin za ta gabatar da shirin shekaru 3 na aiwatar da burin da sassan biyu ke fatan cimmawa nan da shekarar 2035 a kowane taron dandalin FOCAC da za a gudanar a nan gaba. A matsayin matakan sa kaimi ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, shirin na shekaru 3 zai hade da juna, da kuma mai da hankali ga fannoni daban daban, za kuma a kiyaye daukar matakan bisa tsarin bai daya.

Shu Yuting ta kara da cewa, ma’aikatar za ta yi hadin gwiwa tare da sauran hukumomin da abin ya shafa, don tsara shirin yin ayyuka, da kara yin hadin gwiwa tare da bangaren Afirka, don sa kaimi ga amfanawa jama’ar Sin da Afirka ta hanyar aiwatar da ayyuka 9, da kuma bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka mai inganci. (Zainab)