logo

HAUSA

Masanin Sin: Muhimman ayyuka tara za su taimakawa Afrika

2021-12-01 15:44:34 CRI

Masanin Sin: Muhimman ayyuka tara za su taimakawa Afrika_fororder_sin

Muhimman ayyuka tara na hadin gwiwar Afrika da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a cikin jawabinsa, yayin bikin bude taron ministoci na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC karo takwas, sun yi matukar janyo hankalin al’ummun kasa da kasa. Liu Hongwu, shugaban kwalejin nazarin al’amurran Afrika dake jami’ar horaswar malamai ta lardin Zhejiang na kasar Sin, ya bayyana a yayin zantawa da wakilin CMG cewa, muhimman ayyukan tara sun kara nuna cewa, hadin gwiwar Sin da Afrika tana dora muhimmanci wajen biyan muradun kasashen Afrika, da inganta zaman rayuwar al’ummar nahiyar, gami da bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a nan gaba.

Liu Hongwu ya ce, muhimman ayyukan tara sun kara nuna cewa duk halin tsanani da aka shiga game da bunkasa hadin gwiwar Sin da Afrika, bangarorin biyu za su iya lalibo sabbin dabarun tattauna hadin gwiwarsu da kuma gabatar da sabbin kudurorin da za su kyautata huldar dake tsakanin Sin da Afrika.(Ahmad)