logo

HAUSA

Matakan Sin za su yi tasiri wajen kandagarkin nau’in Omicron na COVID-19

2021-12-01 10:52:52 CRI

Matakan Sin za su yi tasiri wajen kandagarkin nau’in Omicron na COVID-19_fororder_病毒-3

Hukumar kula da lafiya ta kasar Sin, ta ce matakai da dabarun da kasar Sin ke amfani da su wajen yaki da COVID-19 za su yi tasiri kan sabon nau’in cutar na Omicron.

Kakakin hukumar, Mi Feng, ya shaidawa manema labarai cewa, kasar Sin za ta nace kan matakai da dabarunta na kandagarki, wadanda ke da nufin dakile shigowar cutar daga ketare da kare sake barkewarta a cikin gida.

Shi ma wani jami’in hukumar, Wu Liangyou, ya ce hukumar lafiyar ta karfafa matakan sa ido da bibiya da nufin gano cutar a kan lokaci da kuma jinyar wadanda suka kamu. (Fa’iza Mustapha)