logo

HAUSA

Firaministan Sin ya bukaci a karfafa matakan kandagarki da jinyar masu dauke da cutar HIV/AIDS

2021-12-01 10:47:10 CRI

Firaministan Sin ya bukaci a karfafa matakan kandagarki da jinyar masu dauke da cutar HIV/AIDS_fororder_AIDS

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bukaci a karfafa matakan kandagarki, da jinyar masu dauke da cutar HIV/AIDS. Kiran na firaminista Li na zuwa ne, gabanin ranar kasa da kasa ta yaki da cutar HIV/AIDS karo na 34, wadda za a gudanar da bikin ta a Larabar nan.

Li Keqiang, wanda kuma mamba ne a zaunannen kwamiti na hukumar siyasa a kwamitin kolin JKS, ya ce an cimma manyan nasarori a ayyukan kandagarki da shawo kan wannan cuta a kasar Sin, ya kuma jaddada muhimmancin mayar da kare rayukan al’umma gaban komai, da kuma inganta ayyukan dake da nasaba da hakan.

Li ya ce akwai bukatar fifita matakan kandagarki, tare da tsara dabarun hade jinyar masu dauke da cutar a sauran ayyukan kandagarkin cutar.  (Saminu)