logo

HAUSA

CMG ya tattauna da mataimakiyar shugaban kungiyar nazarin kirkire-kirkire da manufofin bunkasuwa ta kasar Sin

2021-12-01 20:43:28 CRI

CMG ya tattauna da mataimakiyar shugaban kungiyar nazarin kirkire-kirkire da manufofin bunkasuwa ta kasar Sin_fororder_1201-02

CMG ya tattauna da mataimakiyar shugaban kungiyar nazarin kirkire-kirkire da manufofin bunkasuwa ta kasar Sin_fororder_1201-03

A yau ne, wakilin CMG ya yi hira da mataimakiyar shugaban kungiyar nazarin kirkire-kirkire da manufofin bunkasuwa ta kasar Sin Xu Weixin a taron kasa da kasa na fahimtar kasar Sin na shekarar 2021 da ke gudana daga ranar 1 zuwa 4 ga wannan wata a birnin Guangzhou.

Xu Weixin ta bayyana cewa, dalilin da ya sa kasar Sin ta samu bunkasuwa cikin shekaru fiye da 40 da suka gabata shi ne jagorancin jam’iyyar kwaminis ta Sin. Sin tana da wata taswirar da ta tsara na gudanar da ayyuka, kuma dukkan jama’ar kasar Sin sun yi kokari tare don cimma burin da kasar dake fatan cimmawa. A ganinta babu wasu kasashe a duniya da suka taba yin irin wannan aikin da al’ummar kasar Sin ta yi har na tsawon shekaru fiye da 10.

Game da yadda kasar Sin za ta iya fuskantar barazanar daga sauran kasashen duniya a sakamakon babban ci gaban da ta samu, Xu Weixin ta yi nuni da cewa, Sin ba ta taba tada yake-yake a sauran kasashen waje a tarihi ba, Sin ta tura wakilai zuwa wasu kasashe don sada zumunta da yin hadin gwiwa tare, ta kuma samar wa sauran kasashen duniya fasahohi da ilmi. A baya, Sin ta yi hakan, kuma a yanzu da kuma a nan gaba Sin za ta ci gaba da yin irin wannan aiki. (Zainab)