logo

HAUSA

Antonio Guterres: Tsarin bai daya na rigakafin COVID-19 ne mafita

2021-12-01 09:56:20 CRI

Antonio Guterres: Tsarin bai daya na rigakafin COVID-19 ne mafita_fororder_古特雷斯

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce hanya daya tilo ta ganin bayan annobar COVID-19 a dukkanin sassan duniya ita ce aiwatar da cikakken shirin rigakafi na bai daya.

Mr Guterres, wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, yayin taron ministocin wajen kasashe mambobin kungiyar G77 da Sin, wanda ya gudana a helkwatar MDDr na birnin New York, ya ce har yanzu annobar COVID-19 na ci gaba da addabar dukkanin duniya, ciki har da kasashe masu ci gaba da masu tasowa.

Ya ce MDD na goyon bayan shirin gudanar da rigakafi da hukumar lafiya ta duniya WHO ta tsara, wanda ya kunshi yiwa a kall kaso 40 bisa dari na al’ummun duniya rigakafin cutar nan da karshen shekarar nan, da kuma kara adadin zuwa kaso 70 bisa dari nan da tsakiyar shekarar 2022 dake tafe.  (Saminu)