logo

HAUSA

Ikenna Emewu: Yadda Sin ke kare tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban ya bayar da gudummawa ga ci gaban cinikin kasashen duniya

2021-12-01 11:42:51 CRI

Ikenna Emewu: Yadda Sin ke kare tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban ya bayar da gudummawa ga ci gaban cinikin kasashen duniya_fororder_2934349b033b5bb5f64c34c14caea930b700bcf8

A bana ne ake cika shekaru 20 da shigar kasar Sin kungiyar cinikayya ta duniya WTO. Dangane da wannan batu, babban editan mujallar “Africa China Economy” ta Nijeriya, Ikenna Emewu ya bayyana cewa, cikin wadannan shekaru 20, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kare tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, lamarin da ya ba da gudummawa matuka a fannin raya cinikayyar kasashen duniya.

Ya ce, kasar Sin ta kuma nuna goyon baya ga Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka wajen raya harkokin masana’antu, matakan da suka ba da taimako ga kasashen Afirka wajen habaka kasuwannin kasa da kasa.

Ikenna Emewu ya ce,

“Idan kasashen Afirka sun kyautata harkokin ciniki ta hanyar habaka masana’antun kere-kere, hakan zai tallafa wa Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka. Shi ya sa, ba kawai batun ya shafi kungiyar WTO da cinikin kasashen duniya, har ma, yana da muhimmanci wajen raya harkokin ciniki tsakanin kasashen Afirka, kuma wannan ita ce, babbar gudummawar da kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka, a yayin da take kokarin taimakawa kasashen nahiyar a fannin raya harkokin masana’antu. Da farko ya kamata kasashen Afirka su habaka harkokin ciniki cikin kasashensu kansu da farko, sa’an nan, su mai da hankali kan kasuwannin kasashen duniya. Kasancewar a halin yanzu, kasashen Afirka ba su kware sosai ba a fannin samar da kayayyaki, shi ya sa, nake son yabawa kasar Sin dangane da kokarin da ta yi wajen goyon bayan kasashen Afirka a fannin raya harkokin masana’antu.” (Mai Fassarawa: Maryam Yang)