logo

HAUSA

Iran: Mahalarta shawarwarin Vienna sun amince da baiwa batun takunkumi fifiko

2021-12-01 10:01:23 CRI

Wakilai daga kasashen yamma masu ruwa da tsaki a batun yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran ta shekarar 2015, sun amince da baiwa batun  takunkumin da aka kakabawa Iran fifiko, yayin tattaunawar da suka fara a birnin Vienna.

Da yake tabbatar da hakan a jiya Talata, yayin wani shirin talabijin da wata kafar Iran din ta watsa, game da abubuwan da suka faru a rana ta farko ta zaman na birnin Vienna, mai shiga tsakani na kasar Iran a tattaunawar Ali Bagheri Kani, ya ce ko shakka babu, warware batun haramtaccen takunkumin da aka kakabawa Iran na kan gaba, cikin ajandar kwamitin hadin gwiwar dake tattaunawa, kuma an amince da hakan.

Ali Bagheri Kani, ya ce an cimma nasara a zaman taron na ranar Litinin, kuma ya zama wajibi a jinjinawa kasashen Sin da Rasha, bisa cikakken goyon bayan su ga matsayar Iran.  (Saminu)