logo

HAUSA

Xi da Thongloun za su halarci bikin bude layin dogo na Sin zuwa Laos ta kafar bidiyo

2021-12-01 12:10:26 CRI

Babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai gana da Thongloun Sisoulith, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar LPRP, kana shugaban kasar Lao, inda za su gana ta kafar bidiyo a ranar Juma’a, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a yau Laraba.

Hua ta ce, shugaba Xi da Thongloun za su halarci bikin bude layin dogo tsakanin Sin zuwa Laos ta kafar bidiyo.(Ahmad)