logo

HAUSA

Shugabannin Afrika: Kasashen Afrika da Sin za su kara kaimi don cimma burin samun wadata tare

2021-11-30 10:55:27 CRI

Shugabannin Afrika: Kasashen Afrika da Sin za su kara kaimi don cimma burin samun wadata tare_fororder_FOCAC

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya bayyana cewa, kasashen Afrika da kasar Sin za su kara azama a kokarin cika burinsu na samun wadata tare, domin kyautata zaman rayuwar al’ummun Afrika da Sin.

A jawabin da ya gabatar na bude taron ministoci na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC karo na takwas, wanda aka bude a ranar Litinin, Sall ya bayyana cewa, kasar Senegal tana matukar farin cikin karbar bakuncin wannan muhimmin taro bayan shekaru uku da aka shirya taron kolin FOCAC na Beijing, domin kara zurfafa hadin gwiwa da kyakkyawar abota da kuma dadadden zumuncin dake tsakanin Sin da Afrika.

Shugaba Sall ya ce, taken taron shi ne “Zurfafa hadin gwiwar Sin da Afrika da ingiiza ci gaba mai dorewa don gina kyakkyawar makomar al’ummun Sin da Afrika a sabon zamani", taron ya zo a daidai lokacin da ya dace bisa la’akari da sauye sauyen da ake kara samu da kuma kalubalolin dake addabar duniya wadanda suka zama tilas ga kasashen Afrika da Sin su jure ta hanyar zurfafa huldar siyasa da nuna goyon baya ga juna ta fannin tattalin arziki.

Shugaban kasar jamhuriyar demokaradiyyar Kongo, Felix Tshisekedi, wanda kuma shi ne shugaban karba karba na kungiyar tarayyar Afrika AU, a jawabin da ya gabatar a wajen taron ta kafar bidiyo, ya bayyana cewa, taron FOCAC, ta hanyar muhimmiyar tattaunawa ta gaskiya, zai mayar da hankali ne wajen bibiyar nasarorin da aka cimma a shekaru da dama da suka gabata, tare da bayyana muhimman bangarorin kara yin hadin gwiwar Sin da Afrika nan da wasu shekaru uku masu zuwa.

Azali Assoumani, shugaban kasar Comoros, shi ma a nasa jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, ya bayyana cewa, nasarorin da aka cimma masu cike da tarihi na hadin gwiwar dake tsakanin Afrika da Sin ba batu ne da za a iya yin jayayya kansu ba, kuma abin alfahari ne ga kasashenmu. Ya ce goyon bayan juna ta bangaren samar da zaman lafiya da tsaro, da yaki da fatara, da batun yaki da matsalar sauyin yanayi, sakamakon da aka samu na wadannan hadin gwiwar sun kasance masu faranta rai.(Ahmad)