logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya aike da sakon taya murna ga taron ranar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu

2021-11-30 11:08:57 CRI

Shugaban kasar Sin ya aike da sakon taya murna ga taron ranar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu_fororder_211130-Xi-Faeza3

Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga taron da aka yi a MDD jiya, domin ranar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu ta duniya.

Cikin sakonsa, Xi Jinping ya ce batun Falasdinu na da muhimmanci a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya ce ingantacciyar mafita bisa adalci kuma mai dorewa, da zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra’ila da ci gaba na bai daya ga kasashen Larabawa da Yahudu, ya dace da muradun Falasdinu da Isra’ila, da kuma dadadden burin tabbatar da zaman lafiyar yankin da fatan dukkan kasashe dake kaunar zaman lafiya da adalci.

Ya ce dole ne warware batun Falasdinu ya yi daidadi da ka’idoji da alkiblar da ta dace. Yana mai cewa, dole ne kasa da kasa su daukaka adalci da hakuri da fahimtar juna, su kuma dauki cikar taron zaman lafiya na Madrid shekaru 30 da gudana, a matsayin wata dama ta samar da karin taimako ga komawa teburin sulhu ga Falasdinu da Isra’ila bisa tushen kafa kasashe biyu. (Fa’iza Mustapha)