logo

HAUSA

Jakadan Nijeriya dake Sin: Ana sa ran karfafa hadin gwiwar harkokin kiwon lafiya tsakanin Sin da Nijeriya

2021-11-30 13:27:23 CRI

Jakadan Nijeriya dake Sin: Ana sa ran karfafa hadin gwiwar harkokin kiwon lafiya tsakanin Sin da Nijeriya_fororder_1

Kwanan baya, jakadan kasar Nijeriya dake kasar Sin Baba Ahmad Jidda, ya jinjinawa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, bisa dandalin taron tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC. Ya kuma yi fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannin kiwon lafiya.

A ranar 29 ga wata, aka bude taron ministocin dandalin taron tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashe Afirka karo na 8 a birnin Dakar, fadar mulkin kasar Senegal. Kafin taron, Baba Ahmad Jidda ya ce, bana, shekara ce ta karshen da fara aiwatar da “Manyan Matakai Takwas” da aka gabatarwa a taron FOCAC na shekarar 2018. Cikin shekaru uku da suka gabata, kasar Sin da kasashen Afirka sun cimma sakamako da dama, kamar kafuwar cibiyar nazarin harkokin Sin da Afirka a shekarar 2019, wadda ta samar da dabaru da masana da yawa wajen raya hadin gwiwar sassan biyu.

Haka kuma, ya ce, bisa dandalin FOCAC, Sin da Nijeriya sun habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni da dama, wadanda suka tallafawa al’ummomin kasashen biyu matuka. Kamar gina layin dogo na Abuja-Kaduna, da gina filin jiragen sama na kasa da kasa na birnin Abuja da sauransu. Wadannan matakai sun kyautata zaman rayuwar al’ummomin Nijeriya, yayin karfafa karfin kasar Nijeriya wajen neman bunkasuwa da kanta.

Bugu da kari, jakadan ya kuma yi fatan za a zurfafa hadin gwiwar kiwon lafiya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, ta yadda, dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu za ta ci gaba da samun kyautatuwa bayan kawo karshen annoba. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)