logo

HAUSA

Kasar Sin ta yabawa Afirka ta Kudu wajen musayar bayanai kan Omicron

2021-11-30 19:33:25 CRI

Kasar Sin ta yabawa Afirka ta Kudu wajen musayar bayanai kan Omicron_fororder_Omicron

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fada a yau Talata cewa, ta yaba da yadda kasar Afirka ta Kudu ta yi musayar bayanai a kan lokaci kan sabon nau'in Omicron na annobar COVID-19 da aka gano.

Da yake magana yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa Talatar nan, mai magana da yawun ma'aikatar Zhao Lijian, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya, gami da kasashen kudancin Afirka, domin ganin an yaki cutar.

Zhao ya kara da cewa, ya kamata a yaki cutar ta hanyar kimiyya, sannan kasashe su goyi bayan jagorancin hukumar lafiya ta duniya(WHO).

Zhao ya ce gasar Olympics ta lokacin sanyi za ta ci gaba kamar yadda aka tsara, duk da kalubalen da ke da nasaba da matakan kandagarki da dakile yaduwar cutar. Ya kuma shaida wa manema labarai cewa, kasar Sin tana da gogewa wajen yin rigakafi da dakile annobar COVID-19, ya kuma yi imanin cewa, Sin za ta iya karbar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi kamar yadda aka tsara, cikin lumana da nasara.(Ibrahim)

Ibrahim