logo

HAUSA

Sin da Mozambik sun sha alwashin karfafa hadin gwiwar moriyar juna

2021-11-29 14:29:05 CRI

Sin da Mozambik sun sha alwashin karfafa hadin gwiwar moriyar juna_fororder_1129-Ahmad3-Sin da Mozambique

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da takwaransa na kasar Mozambik, Veronica Macamo, sun yi alkawarin karfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashen biyu a yayin tattaunawar da suka gudanar a babban birnin kasar Senegal.

Mozambik muhimmiyar abokiyar huldar kasar Sin ne a Afrika, Wang ya jaddada cewa, kasar Sin a shirye take ta kara karfafa nuhimmiyar hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Mozambik a fannonin ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa, da aikin gona da kuma makamashi karkashin shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ da dandalin FOCAC da makamantansu domin taimakawa Mozambik don samun ci gaba cikin sauri.

Macamo ya bayyana cewa, Mozambik da Sin a ko da yaushe suna goyon bayan junansu, ya kara da cewa, al’ummar kasar Mozambik suna matukar nuna godiya ga kasar Sin sakamakon taimakon da ta baiwa Mozambik wajen samun ’yancin kanta, kana tallafin da kasar Sin take baiwa Mozambik sun yi matukar bata kwarin gwiwa wajen tsara hanyoyin bunkasa cigaban kasar a nan gaba.

Bangarorin biyu sun kuma bayyana fatansu na yin aiki tare don cimma nasarar gudanar da taron kolin ministoci na dandalin FOCAC karo na takwas, domin samar da sabon kaimi na kyautata hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika. (Ahmad Fagam)