logo

HAUSA

Mahukunta a Tanzania sun bayyana damuwa game da kamfar ruwa da abincin dabbobi sakamakon tsawaitar yanayin fari

2021-11-29 10:14:00 CRI

Mahukunta a Tanzania sun bayyana damuwa game da kamfar ruwa da abincin dabbobi sakamakon tsawaitar yanayin fari_fororder_1129-Saminu3-Tanzania

Mahukunta a Tanzania, sun bayyana matukar damuwa bisa kamfar ruwa, da abincin dabbobi da wasu sassan kasar ke fama da shi sakamakon tsawaitar yanayi na fari.

Gwamnatin Tanzania dai ta alakanta aukuwar hakan da mummunan tasirin sauyin yanayi, wanda ya sabbaba mutuwar tsirrai da ake baiwa dabbobi a matsayin abinci.

Da yake karin haske game da hakan, karamin minista a ofishin mataimakin shugaban kasa, mai lura da harkokin kwadago da muhalli Mr. Seleman Jafo, ya ce yankuna 3 na kasar da matsalar ta fi kamari su ne Dar es Salaam, da Dodoma da Morogoro. Tuni kuma aka fara takaita ruwan da ake turawa wadannan yankuna, a gabar da ake fuskantar karancin sa a koguna da madatsun ruwa. Mr. Jafo ya kara da cewa, akwai rahotanni na mutuwar dabbobi sakamakon kamfar abinci da ruwan sha a yankunan 3.

Jafo ya yi tsokacin ne a birnin Dar es Salaam, yayin gangamin tuka kekune na tsawon kilomita 10, wanda kungiyar tarayyar Turai ta shirya da nufin tallafawa yunkurin gwamnatin kasar, na yayata manufofin kyautata muhalli da dakile tasirin sauyin yanayi.  (Saminu)