logo

HAUSA

Shugabannin AU sun yabawa cikakkiyar huldar dake tsakanin Sin da Afrika gabanin muhimmin taron FOCAC

2021-11-29 10:05:01 CRI

Shugabannin AU sun yabawa cikakkiyar huldar dake tsakanin Sin da Afrika gabanin muhimmin taron FOCAC_fororder_1129-Ahmad1-AU da Sin

Kwamishiniya mai kula da fannin kiwon lafiya, da ayyukan jinkai da kyautata jin dadin al’umma ta kungiyar tarayyar Afrika AU, Amira Elfadil, ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua gabanin fara taron ministoci na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, karo na takwas, wanda zai gudana tsakanin 29 zuwa 30 ga watan nan na Nuwamba a Dakar, babban birin kasar Senegal cewa, godiya ga gwamnatin kasar Sin sakamakon kulla kyakkyawar hadin gwiwa. Godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki dake yin aiki tukuru wajen gina kyakkyawar dangantaka kuma mai karfi tsakanin Sin da Afrika, tsakanin gwamnatin Sin da kungiyar tarayyar Afrika.

Ta bayyana cewa, taron FOCAC na wannan shekarar ya zo ne wasu ’yan kwanaki bayan da hukumar gudanarwar AU ta kammala tsara gina helkwatar cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa wato (Afrika CDC), bisa taimakon kasar Sin, a matsayin wani muhimmin bangare na shirin kula da lafiya wanda aka amince da shi a taron kolin FOCAC na Beijing a watan Satumbar 2018.

Ta ce, muna matukar farin ciki da wannan tabbaci, da wannan hadin gwiwa da kuma karamcin da kasar Sin take nunawa hukumar gudanarwar AU, karkashin tallafin da muke samu a fannin kiwon lafiya, musamman ga sashen cibiyar Africa CDC.

Hukumar AU, musamman ta yaba da hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da Sin a fannin kiwon lafiya bisa yadda take gudana a tsari na moriyar juna, muna bukatar kara karfafa ta.

Amira, ta yabawa gwamnatin kasar Sin a matsayin sahihiyar abokiyar hadin gwiwa kuma mai tabbaci ga kungiyar AU a kokarinta na kyautata ci gaban nahiyar Afrika. (Ahmad Fagam)