logo

HAUSA

Ministan harkokin waje na Sin ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Rasha da India

2021-11-27 16:46:55 CRI

Ministan harkokin waje na Sin ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Rasha da India_fororder_aa18972bd40735fab833adb4adac74ba0d240886

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce yayin da ake fuskantar sauye-sauye a duniya, zabukan da Sin da Rasha da India za su yi, ba muradunsu kadai za su shafa ba, har da inda duniya ta nufa, don haka ya yi kira ga kasashen 3 su lalubo mafita ga rashin tabbas da ake fama da shi a duniya.

Wang Yi ya bayyana haka ne lokacin da ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Rasha da India da aka yi jiya ta kafar bidiyo. .

A cewarsa, a shirye kasar Sin take, ta hada hannu da Rasha da India wajen inganta ruhin bude kofa da hadin kai da aminci, tare da nuna matsayinsu na babbar kasa da kuma zama jagora. (Fa’iza Mustapha)