logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya bukaci kasashen Asiya da Turai su rungumi hadin kai da goyon bayan juna

2021-11-27 16:50:06 CRI

Firaministan kasar Sin ya bukaci kasashen Asiya da Turai su rungumi hadin kai da goyon bayan juna_fororder_a8014c086e061d959d3f3552adec76d862d9ca05

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce kasashen Asiya da Turai, na fuskantar kalubale wajen yaki da annobar COVID-19 da bunkasa farfadowar tattalin arziki, don haka akwai bukatar dukkansu, su rungumi dabara mai karfi ta goyon bayan juna da hadin kai da kuma kwarin gwiwar shawo kan matsaloli.

Li Keqiang, ya bayyana haka ne yayin da ya halarci taron koli karo na 13 na kasashen Asiya da Turai ta kafar bidiyo, wanda ya gudana karkashin Firaministan kasar Cambodia, Samdech Techo Hun Sen.

Firaministan na Sin, ya kuma bayyana cewa, kasashen Asiya da Turai na da mabanbantan tarihi da al’adu da kuma tafarkin ci gaba, saboda haka, ba wani abu ba ne, don sun samu sabanin ra’ayi kan wasu batutuwa. Amma duk da haka, ya kamata dukkan bangarorin su girmama juna, da neman matsaya guda.

Ya kara da cewa, ya kamata dukkan kasashen su daukaka tsarin kasa da kasa karkashin ka’idojin da muradu da dokokin MDD da dokokin kasa da kasa da ka’idojin hulda tsakanin kasa da kasa. (Fa’iza Mustapha)