logo

HAUSA

Kasar Sin ta mikawa Rwanda aikin fadada kwalejin koyon sana'o'i da ta samar da kudin gudanar da shi

2021-11-26 10:33:42 CMG

Kasar Sin ta mikawa Rwanda aikin fadada kwalejin koyon sana'o'i da ta samar da kudin gudanar da shi_fororder_1

A jiya ne, aka kammala aikin fadada ginin cibiyar nazarin koyon sana’o’i ta kasa (IPRC) da ke Musanze, a lardin arewacin kasar Rwanda, a matsayin tallafi da gwamnatin kasar Sin ta samar mata, bayan fiye da shekaru biyu a kammala shi, aka kuma damkawa gwamnatin kasar.

Karamar minista mai kula da harkokin sadarwa na zamani a ma'aikatar ilmi ta kasar Rwanda Claudette Irere ta bayyana cewa, kasar Rwanda na matukar godiya ga kasar Sin.

Irere ta ce, karamcin da Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ta nuna mana, na ba mu wannan matsayi mai girma, wata alama ce ta kyakkyawar abotakanta tsakanin Rwanda da jama'ar kasar Sin.

Irere ta ce tana da kwarin gwiwar cewa, aikin na daya daga cikin irin nasarorin da za su baiwa Rwanda damar koyi da kasar Sin yadda ya kamata. (Ibrahim)

Ibrahim