logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya gabatar da sakon jaje ga takwaransa na Rasha bisa hadarin mahakar Kwal

2021-11-26 20:48:43 CRI

Shugaban kasar Sin ya gabatar da sakon jaje ga takwaransa na Rasha bisa hadarin mahakar Kwal_fororder_0e2442a7d933c8951df2a54e4a6808f9830200ff

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da sakon jaje ga takwaransa na Rasha Vladimir Putin, bisa hadarin mahakar ma’adanin kwal, wanda ya haifar da asarar rayuka da dama.

Shugaba Xi Jinping, wanda ya gabatar da sakon a yau Juma’a, ya jajantawa shugaba Putin, yana mai cewa, ya yi matukar kaduwa bisa jin labarin fashewar iskar gas a mahakar kwal ta Belovo, na yankin Kemerovo.

Shugaban na Sin, ya ce a madadin gwamnati da al’ummar kasar Sin, da kuma shi kan sa, yana mika sakon ta’aziyyar wadanda suka rasa rayukan su ga iyalai da ‘yan uwan su, yana mai jajanatawa gwamnatin Rasha, da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.(Saminu)