logo

HAUSA

Ministocin wajen Sin da Iran sun tattauna ta kafar bidiyo

2021-11-25 11:27:51 CRI

Ministocin wajen Sin da Iran sun tattauna ta kafar bidiyo_fororder_211125-ahmad-4-Sin da Iran

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, a ranar Laraba ya tattauna da takwaransa ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amir Abdollahian ta kafar bidiyo, inda suka tattauna game da dangantaka da kuma hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

A bana ake cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Iran, Wang ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Iran don aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwa da suka tsara, da kuma daga matsayin dangantakar dake tsakaninsu domin cimma sabbin nasarori karkashin muhimmiyar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Iran.

Wang ya ce, batun da ake kira wai taron kolin demokaradiyya wanda Amurka ta gabatar da shi, manufarsa shi ne, neman kawo rarrabuwar kawuna a duniya ta hanyar fakewa da demokaradiyya, da karfafa gwiwar manufofin yin fito na fito, da kuma neman kakabawa sauran kasashen duniya salo irin na Amurka domin neman cimma muradun kashin kai na Amurkar. Wannan manufa ta ci karo da yanayin da duniya ke ciki a halin yanzu, kuma babu wani tasiri da za ta kara yi a nan gaba.

A nasa bangaren, Abdollahian ya ce, muhimmiyar dangantakar dake tsakanin Iran da Sin ta kara ingiza kyakkyawar alakar dake tsakaninsu zuwa sabon matsayi. Iran a shirye take ta zurfafa mu’amalarta da kuma hadin gwiwarta da kasar Sin a dukkan fannoni. Iran tana adawa da manufar nuna ra’ayin bangare guda, da muzgunawa, da yin baki biyu, da kuma yin shisshigi ga ikon da kasar Sin ke da shi kan yankunanta da yi mata katsalandan a harkokin cikin gidanta. (Ahmad)