logo

HAUSA

Firaministan Sin zai halarci bikin bude taron AALCO karo na 59

2021-11-25 20:33:41 CRI

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, zai halarci bikin bude taron kungiyar tuntuba ta masu ruwa da tsaki a fannin shari’a na nahiyar Asiya da Afirka ko AALCO a takaice ta kafar bidiyo.

A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, za a gudanar da taron karo na 59 ne a yankin Hong Kong na kasar Sin, kuma firaminista Li Keqiang zai halarta daga birnin Beijing, zai kuma gabatar da jawabi. (Saminu)