logo

HAUSA

Najeriya za ta sake farfado da jiragen gwamnati a shekarar 2022

2021-11-25 13:40:02 CRI

Najeriya za ta sake farfado da jiragen gwamnati a shekarar 2022_fororder_211125-ahmad-6

Gwamnatin Najeriya ta sanar a ranar Laraba cewa, tana sa ran farfado da kamfanin jiragen saman gwamnatin kasar bayan shafe tsawon shekaru ba ya aiki, kamfanin zirga-zirgar jirgin sama na kasar na Air Nigeria, zai fara aiki nan da watan Afrilun 2022 bayan gudanar da wasu sauye sauye tare da amincewa ga kamfanin jiragen saman kasar ya ci gaba da aiki.

Daga cikin shirin, an tsara dawo da ayyukan jiragen kasuwanci na kasar, wadanda suka dena aiki a shekarar 2012 sakamakon kalubalolin, taron majalisar ministocin kasar dake gudana a duk mako ya amince da wannan kudiri, kamar yadda Hadi Sirika, ministan sufurin jiragen saman Najeriya ya bayyanawa manema labarai a Abuja.

A cewar ministan, wani kamfani ne zai dauki nauyin tafiyar da jiragen saman kasar inda gwamnatin Najeriya za ta dauki kaso 5 bisa 100, wasu kamfanonin kasar za su karbi kaso 46 bisa 100, yayin da raguwar kashi 49 an tanade su domin wani muhimmin tsari na abokan hulda a nan gaba, wadanda suka hada da masu zuba jari na kasashen ketare.

Sirika ya ce, idan kamfanin jiragen kasar ya fara aiki, za a samar da guraben ayyukan yi sama da 70,000. (Ahmad)