logo

HAUSA

Sin na fatan kasashe masu ruwa da tsaki za su fahimci ainihin yanayin hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka

2021-11-25 21:20:58 CRI

Sin na fatan kasashe masu ruwa da tsaki za su fahimci ainihin yanayin hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka_fororder_W020211125705609938828

Yayin taron manema labarai na Alhamis din nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana fatan kasar Sin, na ganin daukacin kasashe masu ruwa da tsaki, sun fahimci irin kyawun hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka.

Zhao ya yi wannan tsokaci ne, yayin da wani dan jarida ya tambaye shi, game da sukar da ministan wajen kasar Faransa Jean-Yves Le Drian ya yi wa hadin gwiwar dake wakana tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, a lokacin zantawarsa da kafar Le Monde.

Zhao Lijian ya ce ya lura da rahotanni masu nasaba da wannan batu, sai dai kuma kalaman na ministan wajen Faransa ba su da wani tushe. Don haka kasar Sin ke mamakin jin su.

Zhao Lijian ya kara da cewa, taro karo na 8 na ministocin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC zai gudana a kasar Senegal. Kuma a yanzu haka, jagororin Afirka, da ministocin wajen kasashen nahiyar na ci gaba da dakon zuwan lokacin taron. Wannan kuma wata shaida ce mai karfi, dake nuni ga yadda nahiyar Afirka ke dora muhimmanci, da tallafawa hadin gwiwar sassan biyu.

Zhao ya ce har kullum Sin na bude kofofin ta, tana kuma maraba da dukkanin sassan kasa da kasa wajen gudanar da hadin gwiwa da Afirka. Kaza lika tana da burin taimakawa sassan kasa da kasa, wajen kafa hadin kai mai karfi don ingiza ci gaban nahiyar Afirka.

Daga nan sai ya yi fatan kasashe masu ruwa da tsaki, za su nazarci alakar dake tsakanin Sin da nahiyar Afirka da idon basira, su kuma saurari muryoyin abokai na Afirka, tare da gudanar da ayyukan ci gaban nahiyar a zahiri.  (Saminu)