logo

HAUSA

Sin ta bayyana matukar adawar ta ga takunkumin da Amurka ta kakabawa wasu kamfanonin kasar 12

2021-11-25 20:32:46 CRI

Sin ta bayyana matukar adawar ta ga takunkumin da Amurka ta kakabawa wasu kamfanonin kasar 12_fororder_edc497c5b6cc09514b0a819b8cd52efd

Kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin Shu Jueting, ta ce gwamnatin Sin ta bayyana matukar adawar ta ga takunkumin da Amurka ta kakabawa wasu kamfanonin ta 12, kuma tuni Sin din ta mika koken hakan ga tsagin Amurka.

Shu Jueting ta bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na yau Alhamis, lokacin da aka gabatar mata da tambaya kan hakan. Ta ce Amurka tana fakewa da sunan tsaro wajen kakaba takunkumi maras tushe ga kamfanonin Sin.   (Saminu)