logo

HAUSA

Sin ta yi taron gabatarwa kasashen Afrika ruhin taron cikakken zama na 6 na kwamitin tsakiyar JKS karo na 19

2021-11-25 14:23:54 CRI

Sin ta yi taron gabatarwa kasashen Afrika ruhin taron cikakken zama na 6 na kwamitin tsakiyar JKS karo na 19_fororder_46ea64a480e34686969ca6bb4eb32e6b

Jiya Laraba, hukumar kula da aikin tuntubar jam’iyyun siyasan kasashen waje ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi taro ta kafar bidiyo don gabatarwa kasashen Afrika ruhin cikakken zama na 6 na kwamitin tsakiyar JKS karo na 19. Shugabanni da matasa fiye da 200 daga jami’iyyu fiye da 50 na kasashen Afrika sama da 40 suka halarci taron.

Shugaban hukumar Song Tao ya bayyana babbar ma’anar taron da kuma kudurorin da taron ya zartas, kuma ya jaddada matsayin da Sin take dauka wato mai da moriyar jama’a a gaban kome. JKS na mai da hankali matuka kan tuntuba da koyi da juna da jam’iyyun kasashen Afrika, yana mai fatan matasan bangarorin biyu za su nuna himma da gwazo wajen hadin kan bangarorin biyu, don taka rawa ga bunkasuwar bangarorin biyu a sabon zamani.

Wakilan kasashen Afrika mahalarta taron sun nuna cewa, hanyar da Sin take bi na zamanantar da al’umma ta habaka hanyoyin da kasashe masu tasowa za su bi ciki har da kasashen Afrika, suna fatan kara yin mu’ammla da JKS don bude wani sabon babi na huldar abokantaka tsakanin bangarorin biyu. (Amina Xu)