logo

HAUSA

Iraki ta umarci dakarun kasashen waje su bar kasar nan da kwanaki 15

2021-11-25 11:36:20 CRI

Iraki ta umarci dakarun kasashen waje su bar kasar nan da kwanaki 15_fororder_211125-ahmad-5-Iraki

Dakarun kawance na kasar Iraki (JOC), a ranar Laraba sun umarci sojojin kasashen waje dake kasar da su fice daga kasar Iraki nan da kwanaki 15, in ba da wasu daga cikin masu ba da shawara dake taimakawa sojojin kasar Iraki.

Kakakin rundunar sojojin ta JOC, Tahseen al-Khafaji, ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran kasar Iraki cewa, kawo karshen zaman dakarun kasashen wajen yana daga cikin manufofin da aka riga aka tsara, kuma babu wasu sauran sansanoni sojoji da dakarun kasashen waje za su iya ci gaba da zama cikinsu in ban da sansanin sojoji na Ayn al-Asad dake yammacin lardin Anbar.

Ya kara da cewa, an tanadi wani tsari na mika makamai da kayan aiki ga sojojin kasar Iraki.

A watan Yuli, kasashen Amurka da Iraki sun gudanar da wani muhimmin taron tattaunawa, a lokacin taron kasashen biyu sun cimma matsayar janye dukkan dakarun Amurka daga kasar Iraki ya zuwa ranar 31 ga watan Disamba. (Ahmad Fagam)