logo

HAUSA

Hukumar ciniki ta Sin ta gabatar da muhimmiyar takardar shirin ba da jagoranci ga aikin cinikin waje

2021-11-25 14:23:22 CRI

Kwanan baya, hukumar ciniki ta kasar Sin ta gabatar da takardar shirin hangen nesa a fannin bunkasa cinikin waje mai inganci na babban shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14. Takardar hangen nesa kan bunkasa cinikin waje mai inganci nan da shekarar 2035, inda ta gabatar da cewa, Sin za ta kara karfin bunkasa yin ciniki da kasashen waje a duk fannoni a cikin wadannan lokuta. Mataimakin ministan hukumar Ren Hongbin ya shedawa manema labarai a jiya Laraba cewa, hukumar za ta gabatar da jerin matakan ba da tabbaci ga cinikin waje kan lokaci don tabbatar da gudanar da wannan aiki yadda ya kamata. Ya ce:

“Shirin zai zurfafa aikin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha da tsare-tsaren hanyoyin da za a bi. Kuma za a bullo da wasu manyan matakai 10 cikin muhimman ayyuka da kasar za ta yi nan gaba, ciki har da yin ciniki ba tare da gurbata muhalli da gudanar da ciniki ta yanar gizo da hada cinikin gida da na waje tare da dai sauransu. A hannu guda kuma, za a habaka wannan aiki bisa halin da ake ciki yanzu, da karawa kamfanonin kwarin gwiwa wajen bunkasa cinikin waje ta hanyoyi daban-daban.” (Amina Xu)