logo

HAUSA

WHO: Sabbin alkaluman masu kamuwa da annobar COVID-19 na ci gaba da karuwa a duniya

2021-11-24 10:36:55 CRI

WHO: Sabbin alkaluman masu kamuwa da annobar COVID-19 na ci gaba da karuwa a duniya_fororder_1124-annoba-Ahmad

A ranar 23 ga wata, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta fitar da rahotonta na mako mako game da annobar COVID-19.

A makon da ya gabata, an samu adadin sabbin masu kamuwa da COVID-19 kusan miliyan 3.6 a duk fadin duniya, kuma sama da mutane 51,000 cutar ta kashe, hakan ya nuna adadin yana cigaba da karuwa a cikin sama da wata guda. Idan an kwatanta da makonnin baya, adadin sabbin masu kamuwa da kuma wadanda suka mutu a duk duniya a makon jiya ya karu da kashi 6%. Daga cikinsu, adadin sabbin masu kamuwa da cutar a Turai ya karu da kashi 11%, kuma adadin alkaluman Turai shi ne mafi girma a duk duniya. Sabbin alkaluman da aka samu a kudu maso gabashin Asiya da gabashin Mediterranea ya ragu da kashi 11% da kuma 9% kowannensu. Sabbin alkaluman wadanda suka mutu a yammcin Pacific da Amurka yayi matukar karuwa a makon jiya, inda ya karu da kashi 29% da kuma kashi 19% kowannensu. A Afrika da kudu maso gabashin Asiya, sabbin masu mutuwa daga cutar ya ragu da kashi 30% da kuma 19% kowannensu.

Kasashe biyar da aka samu adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar a makon jiya, sune Amurka, Jamus, Birtaniya, Rasha da kuma Turkiyya. (Ahmad)