logo

HAUSA

Sin: Ba za a bar wani ko wasu su raba yankin kasa ba

2021-11-24 14:16:27 CMG

Sin: Ba za a bar wani ko wasu su raba yankin kasa ba_fororder_1124-Taiwan-Ibrahim

Mai magana da yawun ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin Zhu Fenglian, ta bayyana yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa Larabar nan cewa, shugaba Xi Jinping ya yi wa Amurka karin haske, kan matsayar kasar Sin game da batun Taiwan, a yayin ganawar farko ta bidiyo da shugabannin kasashen biyu suka yi cewa, manufar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyin hadin gwiwar Sin da Amurka guda uku, su ne tushen siyasa kan dangantakar Sin da Amurka. Gwamnatocin Amurka da suka gaba, sun yi alkawuran martaba wannan manufa. Haka kuma kudurin MDD mai lamba 2758 ko kuma shawarwarin hadin gwiwa guda uku tsakanin Sin da Amurka,duk sun bayyana matsayinsu karara kan batun Taiwan, da matsayin manufar kasar Sin daya tak, wato kasar Sin daya ce kawai a duniya, kana Taiwan, wani bangare ne na kasar Sin, sannan gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ita ce kadai gwamnati bisa doka da ke wakiltar kasar Sin.

Zhu Fenglian ta jaddada cewa, manufar kasar game da Taiwan, a bayyana take kuma ba ta canja ba. Dangane da dangantakar dake tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan kuwa, marbata manufar kasar Sin daya tak, na nufin cewa, Sin daya ce tak a duniya, kuma babban yankin kasar Sin da Taiwan na kasar Sin daya ne, kuma babu wanda zai iya raba ikon mallakar kasar Sin da cikakkun yankunan kasar. A don haka, a shirye ake a yi kokari don sake dinkuwar kasa baki daya cikin lumana. Haka kuma, babu wata makawa a yunkurin kare ikon mallakar kasa da cikakkun yankunan kasar, kuma ba za a taba kyale wani ko wasu su iya raba yankin kasar daga babban yankin kasa ba.(Ibrahim)

Bello