logo

HAUSA

CMG da yankin musamman na Macao sun kulla hadin gwiwar watsa shirye shirye

2021-11-24 21:45:37 CRI

CMG da yankin musamman na Macao sun kulla hadin gwiwar watsa shirye shirye_fororder_微信图片_20211124220220

A yau Laraba 24 ga watan Nuwamban nan ne, kamfanin gungun kafofin watsa labarai na kasar Sin CMG, da takwaransa na yankin Macao, suka sanya hannu kan takardar hadin gwiwa a birnin Guangzhou na kasar Sin.

Bisa takardar, CMG ta baiwa kafar ta talabijin da radio dake yankin musamman na Macao, damar watsa shirye shiryen gasar Olympic ta lokacin hunturu ta birnin Beijing dake tafe, kan tashar cctv-16.

Kaza lika ta kuma samu damar watsa shirye shirye game da gasar kasa da kasa ta Chengdu wadda daliban jami’o’i za su gudanar a lokacin bazara na shekara mai zuwa.