logo

HAUSA

Sin na matukar adawa da gayyatar da Amurka ta yi wa jagororin Taiwan zuwa taron “Dimokuradiyya”

2021-11-24 20:33:13 CRI

Sin na matukar adawa da gayyatar da Amurka ta yi wa jagororin Taiwan zuwa taron “Dimokuradiyya”_fororder_48540923dd54564e7be449911a91e58bd0584f6a

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya jaddada matsayar kasar Sin, na Allah wadai da gayyatar da Amurka ta yiwa jagororin yankin Taiwan, zuwa abun da Amurkar ta kira wai taron kolin dimokuradiyya.

Zhao wanda ya yi wannan tsokaci a Larabar nan, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa, ya ce cikin sassan da Amurka ta gayyata zuwa wannan taro har da wakilan yankin Taiwan. To sai dai kuma a cewar jami’in na Sin, ya zama wajibi a sani cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin, ita ce kadai halastacciyar gwamnati dake wakiltar daukacin kasar Sin, kuma yankin Taiwan bangare ne na Sin, yayin da kuma manufar kasar Sin daya tak a duniya, tuni ta samu amincewa a matsayin muhimmin jigo na alakar sassan kasa da kasa.

Bugu da kari, Zhao Lijiang ya ce, yankin Taiwan ba shi da wani matsayi na daban a dokokin kasa da kasa, illa kasancewarsa wani bangare na kasar Sin.   (Saminu)