logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta kiyaye muradun kungiyoyin tsiraru yadda ya kamata

2021-11-24 09:40:15 CRI

Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta kiyaye muradun kungiyoyin tsiraru yadda ya kamata_fororder_1124-US-minority groups-Ibrahim

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a jiya Talata cewa, kamata ya yi hukumar Amurka ta dauki matakan da suka dace, don magance matsalar nuna wariyar launin fata, a wani mataki na kiyayewa da tabbatar da hakki da moriyar 'yan tsiraru, ciki har da al'ummar Sinawa dake zaune a kasar.

Zhao Lijian ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, lokacin da aka bukaci ya yi tsokaci kan yadda ake farma Sinawa dake zaune a kasar Amurka. Yana mai cewa, al'ummar kasar Sin sun ba da muhimmiyar gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin Amurka.

Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta kiyaye muradun kungiyoyin tsiraru yadda ya kamata_fororder_1124-US-minority groups-Ibrahim2

Ya ce, duk da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa da aka samu a kasar, abin kunya ne a ce ba a magance matsalar wariyar launin fata da ake nunawa 'yan asalin kasar Sin ba. Maimakon haka ma, ya ce, ta zama wata cuta dake ci gaba da addabar al'ummar Amurka. Ya ce, hakan na da nasaba da yadda Amurka ke yada akidar kin jinin kasar Sin, wadda ta zama ruwan dare gama duniya, don neman bata suna da ma takalar kasar Sin. (Ibrahim Yaya)