logo

HAUSA

Rahoto: Kasar Sin ta yiwa abokan takararta zarra wajen amfani da fasahar zuke iskar makamashin carbon

2021-11-24 14:39:39 CMG

Rahoto: Kasar Sin ta yiwa abokan takararta zarra wajen amfani da fasahar zuke iskar makamashin carbon_fororder_1124-carbon-Sin-Ahmad

Rahoton da jaridar The Times ta kasar Birtaniya ta gabatar ya bayyana cewa, kasar Sin ta sha gaban abokan takararta wajen kirkirar sabuwar fasahar dake tattare iskar da makamashin carbon ke fitarwa, yayin da kasar ta sha alwashin cimma nasarar kudirinta na rage fitar da iska mai gurbata muhalli kafin nan da shekarar 2060.

A shekarar bara, kasar Sin ta samar da kashi 81% na dukkan sabbin wuraren adana iskar carbon din da aka tattara, inda hakan ya baiwa kasar damar zama kan gaba a duniya a matsayin kasar da tafi kowace kasa samar da sabbin fasahohin tattare iskar da makamashin carbon ke fitarwa, kamar yadda jaridar wacce ke da ofishinta a London ta wallafa cikin sharhin da ta rawaito daga cibiyar BDO, wata cibiyar nazari ta hadin gwiwa mafi girma a duniya, ta bayyana a ranar Litinin.(Ahmad)

Bello