logo

HAUSA

An kashe a kalla fararen hula 10, da Jandarma 9 a wani hari da aka kai a Burkina Faso

2021-11-23 10:29:39 CRI

An kashe a kalla fararen hula 10, da Jandarma 9 a wani hari da aka kai a Burkina Faso_fororder_211123-yaya-4-Burkina Faso

Ministan sadarwa kana kakakin gwamnatin kasar Burkina-Faso, Ousseni Tamboura, ya sanar a jiya Litinin cewa, an kai wani hari a daren ranar Lahadi zuwa Litinin, kan wasu sojojin da ke yankin Foube na lardin Sanmatenga a kasar ta Burkina Faso, lamarin da ya yi sanadin kashe fararen hula a kalla 10 da Jandarmomi guda 9.

Rahotanni na nuna cewa, an kashe Jandarmomi 9 da fararen hula da dama, kamar yadda ministan ya bayyana ta gidan talabijin din kasar.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin. (Ibrahim Yaya)