logo

HAUSA

Kasar Sin ta harba wani sabon tauraron dan adam kan binciken duniya

2021-11-23 10:17:55 CRI

Kasar Sin ta harba wani sabon tauraron dan adam kan binciken duniya_fororder_211123-yaya-1-Gaofen3

A yau ne, kasar Sin ta harba wani sabon tauraron dan adam mai nazarin harkokin da suka shafi duniyarmu, daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin.

An yi amfani da rokar Long March-4C, wajen harba tauraron dan Adam din mai suna Gaofen-3-02, da misalin karfe 7:45 na safe agogon Beijing na kasar Sin, kuma ya shiga falakin da aka tsara cikin nasara.

Wannan shi ne karo na 398 da aka yi amfani da rokar dakon kaya na Long March wajen harba irin wadannan taurarin dan-Adam. (Ibrahim)