logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin ya yi kira da a dauki kwararan matakai don yaki da fataucin kananan makamai

2021-11-23 10:12:41 CRI

Wakilin kasar Sin ya yi kira da a dauki kwararan matakai don yaki da fataucin kananan makamai_fororder_211123-yaya-2

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira da a dauki kwararan matakai don yaki da fataucin kananan makamai. Ya ce, sarrafa kananan makamai yana da tasiri kan zaman lafiya da tsaro. Don haka, yaki da fataucinsu yana da matukar muhimmanci wajen kiyaye ci gaban tattalin arziki da ci gaban zamantakewar dukkan kasashe. Wakilin na kasar Sin ya ce, ya kamata a gaggata karfafa ikon sarrafa makamai bisa tsarin bangarori daban-daban

Ya kuma bukaci kasashen duniya, da su mai da hankali kan fannoni hudu: Na farko shi ne kara karfin ayyukan kasashen da abin ya shafa, da cimma cikakken tsarin sarrafa kanana da manyan makamai, da taimakawa kasashen yanki samun nasarar murmurewa bayan COVID-19, da magance tushen rikice-rikice da matsalolin da ke haifar da rikici da tashe-tashen hankula, da aiwatar da tsauraran takunkumin kwamitin sulhun MDD na hana shigo da makamai, da katse hanyoyin zirga-zirgar kananan makamai ba bisa ka'ida ba, da karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, da kuma baiwa MDD cikakken taka rawa a matsayin babbar kafa.

Zhang Jun ya kara da cewa, ya kamata a rika gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, bisa ka'idojin da aka dora musu, da mutunta ikon kasashen da abin ya shafa, su kuma ba da taimako sosai a fannin samar da ayyukan yi. (Ibrahim Yaya)