logo

HAUSA

Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane da ba a tantance adadinsu ba a yankin arewa maso yammacin Najeriya

2021-11-23 14:23:25 CRI

Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane da ba a tantance adadinsu ba a yankin arewa maso yammacin Najeriya_fororder_211123-yaya-6-Kaduna

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa, an yi garkuwa da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba, bayan da wasu ’yan bindiga suka kai wa motocinsu hari, a kan wata babbar hanya a jihar Kaduna dake yankin arewa maso yammacin Najeriya ranar Lahadi.

Samuel Aruwan, ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai. Yana mai cewa, an kashe wani mutum guda a harin da ’yan bindigar suka kai wa wasu motoci a kan hanyar da ta hada jihar Kaduna da babban birnin tarayyar kasar Abuja, tare da yin garkuwa da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba.

Nan take dai, jami’an tsaro sun garzaya wurin da harin ya faru a karamar hukumar Kachia da ke jihar bayan sun samu sanarwar jami’an tsaro, tare da ceto mutane 11. Ya kara da cewa har yanzu wasu matafiya na hannun ’yan bindigar. .

Aruwan ya kara da cewa, rundunar ’yan sanda ta tura karin jami’ai da kayan aiki domin tabbatar da tsaron matafiya a kan babbar hanyar. Kuma a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro na hadin gwiwa a yankunan jihar dake fama da matsalar tsaro.

A don haka, ya bukaci al’ummar dake kusa da babbar hanyar, da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri, domin su samu damar magance matsalar tsaro dake addabar jihar. (Ibrahim)