logo

HAUSA

Shugaba Putin ya karbi gayyatar halartar bude gasar Olympics ta birnin Beijing

2021-11-23 21:36:39 CRI

Shugaba Putin ya karbi gayyatar halartar bude gasar Olympics ta birnin Beijing_fororder_641

Sakataren watsa labarai na fadar shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov, ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin, ya amshi sakon gayyatar shugaba Xin Jinping na Sin, zuwa halartar bikin bude gasar Olympic ta birnin Beijing ta lokacin hunturu dake tafe a farkon shekara mai zuwa. Mr. Peskov ya ce bayan kasashen biyu sun tattauna dukkanin shirye-shiryen game da hakan, za su fitar da bayanai don gane da batun.

Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya bayyana yayin taron manema labarai na Talatar nan cewa "Wannan gayyata wata al’ada ce mai kyau tsakanin Sin da Rasha, inda tun tuni shugabannin kasashen biyu ke gayyatar junan su zuwa manyan bukukuwa, a duk lokacin da daya daga cikin su za ta karbi bakuncin ta”.

Zhao ya kara da cewa, a shekarar 2014, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya samu gayyata zuwa bikin bude gasar Olympics ta lokacin hunturu da aka gudanar a birnin Sochi na Rasha. A wannan karo kuma, ya gayyaci shugaba Putin zuwa kasar Sin, domin ya halarci bikin bude gasar ta Beijing. Kuma shugaba Putin ya amsa wannan gayyata cike da farin ciki. Har ila yau, sassan biyu na ci gaba da tattaunawa da juna, game da shirye shiryen zuwan shugaba Putin kasar ta Sin. (Saminu)