logo

HAUSA

Lithuania za ta dandana kudarta bisa abun da ta yi na amincewa kafa ofishin wakilcin Taiwan a kasar

2021-11-22 20:49:00 CRI

Lithuania za ta dandana kudarta bisa abun da ta yi na amincewa kafa ofishin wakilcin Taiwan a kasar_fororder_22171011zwrb 拷贝

Kasar Lithuania ta ce wai ofishin wakilcin da yankin Taiwan na kasar Sin ya kafa a kasar, ba shi da wani matsayin da ya shafi diplomasiyya. Amma mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin cewa, wannan furucin jirkita gaskiya ne, kuma dole ne gwamnatin Lithuania ta dauki alhakin abun da ta aikata.

Zhao ya ce, Lithuania ta yi biris da adawar kasar Sin, ta kuma lamuncewa hukumar Taiwan ta kafa ofishin wakilcinta a kasar, al’amarin da ya zamo yunkuri na balle Taiwan daga cikin kasar Sin, kana misali ne mai munin gaske. (Murtala Zhang)