logo

HAUSA

Sin da ASEAN sun kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakaninsu

2021-11-22 11:41:36 CRI

Yau da safe ne a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarta tare da shugabantar taron koli na murnar cika shekaru 30 da kafa dangantakar dake tsakanin Sin da kungiyar kasashen gabashi da kudancin nahiyar Asiya (ASEAN) ta kafar bidiyo

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a yau ne aka sanar da kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin Sin da kungiyar ASEAN a hunkunce, wannan batu ne mai ma’ana matuka a tarihin raya dangantakar dake tsakanin sassan biyu, hakan zai kara sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa da wadata a yankin, da ma duniya baki daya.

Xi Jinping ya bayyana cewa, a cikin shekaru fiye da 30, Sin da ASEAN sun samu nasarori kan hadin gwiwarsu, Sin da kasashen ASEAN suna kusa da juna kuma al’adunsu suna kama da juna, kana dukkan bangarorin biyu, sun zabi hanyar raya dangantakarsu da ta dace da yanayin da ake ciki, wato girmama juna, da hadin gwiwa don samun moriyar juna, da nuna goyon baya ga juna, da kuma fahimtar juna da yin koyi da juna.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta zama sahihiyar kawa ga kungiyar ASEAN a baya da kuma yanzu da ma nan gaba. Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kungiyar ASEAN, ta yadda za ta taka muhimmiya rawa kan harkokin da suka shafi yankin da na kasa da kasa. (Zainab)