logo

HAUSA

Shugaban kwamitin gudanarwar AU ya yaba da yarjejeniyar daidaita rikicin siyasar Sudan

2021-11-22 09:39:48 CRI

Shugaban kwamitin gudanarwar AU ya yaba da yarjejeniyar daidaita rikicin siyasar Sudan_fororder_1122-AU-Sudan-Ahmad

Shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU), Moussa Faki Mahamat, a jiya Lahadi ya yaba da yarjejeniyar baya bayan nan da aka cimma game da warware dambarwar siyasar kasar Sudan.

Shugaban na AU ya nuna gamsuwa da sanya hannu kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugaban majalisar koli ta al’amurran shara’a na kasar Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, da firaministan kasar Abdalla Hamdok.

Mahamat ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin mataki na kokarin maido da dokokin kundin tsarin mulki wanda ke kunshe cikin yarjejeniyar Khartoum, wacce aka amince da ita a ranar 19 ga watan Agustan 2019, wadda ta tsara matakan da za a tabbatar da kafa gwamnatin demokuradiyya a kasar Sudan.

Shugaban na AU ya zaburar da dukkan masu ruwa da tsaki na bangarorin siyasa, da na shugabannin al’umma, da fararen hula, da sojoji, da su kara zurfafa matsayar da aka dauka, kana su taimaka wajen aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, domin a samu ingantaccen yanayin zaman lafiya da hadin kan kasa baki daya.

Mahamat, ya sake yin kira ga al’ummar kasa da kasa da su sake jaddada kudirinsu na goyon bayan kasar Sudan domin ta cimma nasarar maido da zaman lafiya, da yin tsare-tsaren tabbatar da demokaradiyya, domin a samu damar gudanar da zabuka masu inganci kuma cikin ’yanci, wanda a cewarsa ita ce kadai hanyar da za ta kawo karshen rikicin shugabanci da samun ci gaba mai dorewa a kasar. (Ahmad)