logo

HAUSA

Shugaba Xi ya aike da sakon taya murnar bude taron kasa da kasa na kafofin watsa labarai

2021-11-22 21:54:03 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar bude taron kasa da kasa karo na 4, na kafofin watsa labarai wanda aka bude yau Litinin a nan birnin Beijing.

Cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce fatan shi ne baki mahalarta taron za su yi tattaunawa mai zurfi, da bunkasa cimma matsaya game da jigon taron, tare da zamowa masu sada ra’ayoyin al’ummu daban daban, da musayar al’adu. Kana su bada gudummawar ingiza gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil adama. (Saminu)