logo

HAUSA

Rahoton jin ra’ayin al’ummomin Afirka ya nuna cewa Sin ta fi sauran kasashe taka rawa a Afirka

2021-11-22 21:21:58 CRI

Rahoton jin ra’ayin al’ummomin Afirka ya nuna cewa Sin ta fi sauran kasashe taka rawa a Afirka_fororder_1

Kwanan nan ne wata shahararriyar cibiyar jin ra’ayoyin al’umma a nahiyar Afirka, mai suna Afrobarometer, ta fitar da wani rahoto dake nuna cewa, kasar Sin tana kan gaba a duniya wajen taka muhimmiyar rawa a nahiyar Afirka.

A dayan bangaren, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya gabatar da jawabi kwanan nan a hedikwatar ECOWAS, inda ya yi suka game da hadin-gwiwar da kasashen Afirka ke yi da sauran wasu kasashe.

Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya ce, hadin-gwiwar Sin da Afirka, hadin-gwiwa ne na neman cimma moriyar juna, kana abu ne da yake samun karbuwa ga kasashen Afirka.

Mista Zhao ya ce, kasar Sin tana marawa kasashen Afirka baya, don su samu goyon-baya daga sauran wasu kasashe wajen samun ci gaba ta hanyoyi daban-daban. Ra’ayin kasar Sin shi ne, duk wata kasa da take son hada kai da kara yin mu’amala da kasashen Afirka, ya dace ta mutunta zabin al’ummun kasashen, da sauraren ra’ayoyinsu, da kara samar musu da alherai a zahirance, a wani kokari na taimakawa kasashen Afirka farfado da tattalin arziki da samar da ci gaba. (Murtala Zhang)