logo

HAUSA

Jaridar Rasha ta wallafa sharhi mai taken “hadin gwiwar dake tsakanin kafofin watsa labaru ta kara sada zumunta a tsakanin Rasha da Sin”

2021-11-22 11:28:23 CRI

Jaridar Rasha ta wallafa sharhi mai taken “hadin gwiwar dake tsakanin kafofin watsa labaru ta kara sada zumunta a tsakanin Rasha da Sin”_fororder_1122-1

A jiya ne, jaridar Rasha ta wallafa wani sharhi a shafinta na Intanet mai taken “hadin gwiwar dake tsakanin kafofin watsa labaru, ta kara sada zumunta a tsakanin Rasha da Sin”, inda ta yi nuni da cewa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yaba da dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin a yayin taro da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ta shirya a ranar 18 ga wannan wata. Haka kuma a wannan rana,shugaba Putin ya bada umurnin shugaba, inda ya baiwa shugaban babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong lambar yabo ta sada zumunta, saboda gagarumar gudummawar da ya bayar wajen sada zumunta da kara yin hadin gwiwa da fahimtar juna a tsakanin jama’ar Sin da Rasha, wannan ya shaida cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kafofin watsa labaru yana da babbar ma’ana ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab)