logo

HAUSA

An kammala dukkan gwaje-gwaje a yankin da za a gudanar da gasar wasannin Beijing 2022 Olympic

2021-11-22 10:08:12 CRI

An kammala dukkan gwaje-gwaje a yankin da za a gudanar da gasar wasannin Beijing 2022 Olympic_fororder_1122-Olympics-Ahmad

A karshen wanan mako an kammala dukkan gwaje gwajen da suka kamata a yankin da za a shirya gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 Olympic da ta nakasassu, inda gwaje gwaje ya shafi wajen da aka tanadawa mahalarta 2,415, wanda ya kunshi gidajen kwana, da kantunan dafa abinci, da cibiyoyin gwajin annobar COVID-19 (PCR).

A bangaren kudu na cibiyar wasannin Olympic ta kasa, yankin na kunshe da gine gine 20, wanda zai karbi bakuncin mahalarta gasar Olympics kimanin 2,338, da kuma mahalartar gasar nakasassu kimanin 1,040.

Ju Qiang, mataimakin darakta mai kula da sashen gidajen kwana na yankin, ya bayyana cewa, ’yan wasa za su iya daidaita girman gadajensu wajen kara tsawonsu har zuwa mita 2.4 domin su ji dadin barci da samun kyakkyawan hutu.

A cewar Ji Ye, mataimakin daraktan sashen kula da abinci na yankin gudanar da wasanin, yankin zai dinga samar da isasshen abinci ga ’yan wasan a lokacin gudanar da gasar, kuma akwai jadawalin nau’ikan abinci har guda 678 da za a samar ga ’yan wasan da suka fito daga bangarorin al’adu daban daban na duniya, domin biyan muradunsu da kuma yanayin nau’ikan abincin da jikinsu ke bukata, sannan kuma an bayar da kulawa ga tsarin abinci na mabiya addinai daban daban. (Ahmad Fagam)