logo

HAUSA

Masani: Kafa dandalolin Sin da Afrika ya haifar da kyakkyawar makomar Afrika

2021-11-22 10:43:12 CRI

Masani: Kafa dandalolin Sin da Afrika ya haifar da kyakkyawar makomar Afrika_fororder_1122-Sino-Africa-Ahmad

Wani masanin kasar Kenya ya bayyana cewa, hanyoyin bunkasa dangantakar Sin da Afrika, ta hanyar dandalin da FOCAC da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ BRI, ya taimaka wajen samar da kyakkywar makomar ci gaban nahiyar Afrika.

Peter Kagwanja, shugaban cibiyar nazarin manufofin Afrika ya bayyana cikin wani sharhi da aka wallafa a jaridar Sunday Nation dake kasar Kenya inda ya ce, dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC), da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ BRI, tamkar wasu tagwayen injina ne na karfafa cigaban dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika.

Kagwanja ya ce, dandalin FOCAC tamkar wani inji ne na tsara manufofi da tattaunawa da yin tsare tsare, yayin da shawarar BRI ta kasance a matsayin wani inji na samar da kudade da kuma aiwatar da manufofin da aka tsara.

Masanin ya lura cewa, ta hanyar kafa dandalolin, kasar Sin ta tallafawa ayyuka masu yawa kamar aikin gina hanyoyin mota, da layin dogo da tashoshin ruwa wanda ya ratsa dukkan yankuna ya kuma sada kasashen Afrika da junansu. (Ahmad Fagam)