logo

HAUSA

Ƙarfin wutar lantarki na kasar Sin da ake iya sabuntawa ya kai kw biliyan 1

2021-11-22 09:57:26 CRI

Ƙarfin wutar lantarki na kasar Sin da ake iya sabuntawa ya kai kw biliyan 1_fororder_1122-Energy-Ibrahim

Hukumar kula da makamashi ta kasar Sin ta bayyana cewa, ya zuwa karshen watan Oktoban da ya gabata, yawan makamashin da ake iya sabuntawa da kasar ta samar, ya kai kilowatt biliyan 1.002, wanda ya ninka na karshen shekarar 2015.

A cewar bayanai, alkaluman suna wakiltar kashi 43.5 cikin 100 na karfin wutar lantarki da kasar ta samar, wanda ya karu da kashi 10.2 cikin 100 daga karshen shekarar 2015.

Daga cikin jimillar, karfin wutar lantarki bisa karfin ruwa ya kai kilowatt miliyan 385, inda na makamashin iska ya kai kilowatt miliyan 299, bisa hasken rana kuwa ya kilowatt miliyan 282, yayin da karfin wutan da aka samar bisa albarkatun halittu ya kai kilowatt miliyan 35.34.

Hukumar ta ce, wutar lantarki bisa karfi na iska, da albarkatun halittu da ruwa da kasar ta samar ya ci gaba da zama na farko a duniya.

Wata sanarwar da kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwar kasar suka fitar cikin hadin gwiwa ta ce, ya kamata yawan makamashi da bai shafi mai ba, ya karu zuwa kashi 20 cikin dari a cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 14 wato daga shekarar 2021-2025. (Ibrahim Yaya)