logo

HAUSA

Hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin kasuwanci na bunkasa yadda ya kamata

2021-11-21 17:07:35 CRI

Hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin kasuwanci na bunkasa yadda ya kamata_fororder_11

Bisa alkaluman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta fitar kwanan nan, daga watan Janairu zuwa Satumbar bana, hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kasuwanci na kara inganta. Jimillar kudin cinikayyar Sin da Afirka ya kai dala biliyan 185.2, adadin da ya karu da kaso 38.2 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kana, yawan jarin da kasar Sin ta zuba kai-tsaye cikin sana’o’in Afirka ya kai dala biliyan 2.59, wanda ya karu da kaso 9.9 bisa dari idan an kwatanta da na makamancin lokacin bara. Hakan na nuni da cewa hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannin kasuwanci na kara samun murmurewa duk da tasirin annobar COVID-19.

Har wa yau, ana kara lalibo wasu sabbin hanyoyin hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin kasuwanci, ciki har da raya tattalin arziki bisa hanyar sadarwa ta zamani. Gina dandalin cinikayya ta kafar sadarwar intanet, da sayar da kayayyaki ta kafar intanet kai-tsaye, na taimakawa sosai ga gudanar da harkokin kasuwanci tsakanin Sin da Afirka.

A dayan bangaren ma, gina yankunan raya sana’o’i daban-daban shi ma ya zama muhimmin dandalin hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin zuba jari. Akwai kasashen Afirka da dama wadanda suka koyi yadda kasar Sin ta samu nasara wajen jawo jarin waje da bunkasa sana’o’i, inda suka tsara shirye-shiryen nasu na raya yankunan sana’o’i. (Murtala Zhang)