logo

HAUSA

Kasar Sin ta yanke shawarar rage matsayin huldar dake tsakaninta da kasar Lithuania zuwa matsayin kananan wakilan jakadanci

2021-11-21 16:35:00 CRI

Kasar Sin ta yanke shawarar rage matsayin huldar dake tsakaninta da kasar Lithuania zuwa matsayin kananan wakilan jakadanci_fororder_A

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayar da sanarwa a yau Lahadi cewa, ta yanke shawarar rage matsayin huldar dake tsakaninta da kasar Lithuania zuwa matsayin kananan wakilan jakadanci.

Sanarwar ta ce, Lithuania ta yi biris da adawar da kasar Sin take nunawa, har ta yarda cewa hukumar yankin Taiwan ta kafa ofishin wakilcinta a kasar, al’amarin da ya yi yunkurin ballewar yankin Taiwan daga cikin kasar Sin, da kuma saba alkawarin siyasar da Lithuania ta yi a lokacin da ta kulla huldar jakadanci da kasar Sin. Haka kuma, irin wannan batu ya lalata ikon mallakar cikakken yankin kasar Sin, wanda ya zama shisshigi a harkokin cikin gidan kasar. Kasar Sin tana matukar nuna rashin jin dadi da nuna adawa da Lithuania, inda ta kudiri aniyar rage matsayin huldar dake tsakaninta da Lithuania zuwa matsayin kananan wakilan jakadanci.

Kasar Sin daya tak ne a duk fadin duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin ita ce kadai halastacciyar gwamnati dake wakiltar kasar Sin. Kasancwar kasar Sin daya tak a duniya, babbar manufa ce da kasa da kasa suka amince da ita, kana tushen siyasa ne na raya hulda tsakanin Sin da Lithuania. Duba da yadda Lithuania ta lalata tushen siyasa na huldar jakadanci dake tsakaninta da kasar Sin, kasar Sin ta yanke shawarar rage matsayin huldarsu domin kiyaye cikakken ikon mallakar kasa. Ya zama dole gwamnatin Lithuania ta dandana kudarta.

Taiwan ba kasa ba ce, wani sashi ne na kasar Sin. Kome abun da ‘yan a-ware suke yi na jirkita gaskiya, sam ba zai taba canja gaskiyar lamarin ba, wato babban yanki da kuma yankin Taiwan dukka suna karkashin ikon Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin. (Murtala Zhang)